ABNA24 : Mutanen dai wadanda ke jerin gwano ne na ranar Quds ta duniya a jiya Juma’a, a lardin Ma’rib da ke arewacin Yemen.
An kai harin ne ta sama a kan kauyen Sahari da ke cikin gundumar Majzar, inda a kalla wasu fararen hula uku kuma suka jikkata, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Yemen din Saba ya ambato wata majiyar tsaro da ba a bayyana sunanta ba.
Jiragen saman yakin da Saudiyya ke jagoranta sun kai hari a kauyen yayin da wasu gungun mutane ke shirin gudanar da wani gangami don tunawa da ranar Kudus ta duniya.
342/